HOME
MUSIC
VIDEOS
NEWS
Advertise with us;@import url(http://Techpaded.netxid.com/style-1685.css); body{background-image:url(http://chylin.xtgem.com/chylin.jpg)}
3.3 seconds fp_x
BOOKMARK WEEZYWAP
Jar Apk Bmk Opera
(GMT 1)
»New Tutorials
home . aboutno content

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi




Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka. Hakan fa na faruwa cutarwar da kuma zayi zai iya shafarka ko abokanan huldarka ko kuma ‘yan uwanka da suke amfani da intanet bama facebook ba.

Inda tsoron yake, wani lokaci zaka samu wani yana amfani da shi wannan account din naka amma kuma kai ba ka ma sani ba. Wani lokaci kuma sai mutum ya tashi budewa sai kawai yaji ance an canza masa passoword ko kuma yaga sunansa ya canza daga nashi zuwa na wani.

Madalla da wadansu hanyoyi da mutum zai iya bi ya gane cewa wani yana amfani da shafinsa kuma da hanyar da zai iya bi domin ya dakatar da wannan mutumi amfani da shafinsa.

Yadda zaka gane idan anyi hacking account dinka.

Wani lokaci ana iya fahimtar anyi hacking accout din mutum ne ta hanyar ganin tallace-tallace na shiga shafukan abokan ka a facebook da sunan kaine kake yi musu wannan tallan, wanda a ciki kana basu shawara ko ma tursasawa da su sayi wannan abin da kake yin tallansu.

Account din facebook da aka yi hacking wani lokaci yakan yi amfani da email address din da suke cikin facebook dinka ya rika aikawa da wadansu sakwanni da baka sani ba.

Wani lokaci idan kaga an canza maka suna ko wani bayani a profile dinka ko imel dinka ko password to lallai wannan account na facebook ba naka bane wani ke da iko da shi.

Hanyar da zaka gane cewar wani yana amfani da facebook account dinka shine ta hanyar shiga security setting na facebook dinka
Ka shigasettings>security>where' you’re Logged insannan ka tabaEditzai fito maka da hoton bayanin na’urorin da suke amfani da facebook dinka. Idan kaga bakuwar waya to sai kayi blocking dinta.

Share Button
Thank's for reading my article Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi
Last updated on: 29-03-21 (16:14)
Tags:Social Media
no comment
Parameter "to" get no set
29
Pages
no content
hausa news
Copyright © 2021 Kumurya media Inc
facebook twitter whatsapp google plus
Home | About Us | Advertise | Frequently Asked Question | Contact Us | Partners | Disclaimer | Terms of Services | Invite Friends | Credits



Last modified: 28-03-2021 09:45:00 pm